Karya Don Burge Abokai Ko Kawaye Kwalin Adon 'Yan-Zamani

Matasa

Sau nawa mutun kanyi karaya akan cewar ya taba ganin wani fim, alhalin ba haka bane? Ko ya taba karanta wani littafi, duk don ya burge abokan shi, alhali babu wani dalilin yin hakan. Wasu kuma kan dauka cewar idan yace ya kalla fin din ko ya karanta littafin, za’a dauke shi a matsayin wani hadaden gaye.

Haka kuma sau da yawa mutane kan bude kofa irin wadda ake rubuta mata “Full” da nufin cewar a jawo sai kaga mutane suna tura kofar waje. Mafi akasarin masu zanen gidaje ko masu kawatar da gidaje ko ofisoshi basu damuwa da yadda mutane ke tunani, su dai bukatar su kawai ace gurin yayi kyau. Shiyasa da dama mutane kanji kunya idan haka ta faru dasu a lokacin fita ko shiga wani guri.

Sau nawa za kaga matasa don su burge kodai abokan su ko ‘yan-matan su, za kaga suna bin wata waka, wai su don ace sun san wakar kuma sun iya raira abun da ake kira “Lyrics” wato ace mishi ai ya hadu. Babu ma kamar ace kodai wakar tana tashe ko kuma wakar da aka raira ta da turanci ce. Binciken dai ya cigaba da cewar, a lokutta da dama mutane kanyi magana wanda idan kana duba leben su, zaka iya gane ko gaskiya suke fada ko kara.