Tarbiyar Iyaye Nabin 'Yaya Mata A Ko'ina Suke

girls

Balkisu Umar Aliyu. yar asalin jihar sakkwato ce, Ta fara neman ilimi tun tana ‘yar shekaru uku. Ta fara karatun Islamiya domin neman ilimin addinin musulunci. Nan ne tayi saukar Al’kurani mai girma kuma tayi bita sau uku, tareda karatun littafai masu dama. Ta fara karatun firamare a makarantar Muhammad Bankanu. Bayan ta kare taje FGC (Federal Government College Sokoto). Daganan ta samu takaddun kamala sakandire, sai taje Sokoto Polytechnic tayi karatun diploma a fanni gudanar da ayukkan gwamnati wato (Public Administration).

Tayi yunkuri da kokarin neman yin digiri a jami’ar Usman Dan Fodiyo University sokoto, sai kuma ta canza ra’ayin ta wurin neman zuwa karatu kasar waje, domin neman ilimi da budar ido. Ta nemi zuwa kasashe daban daban, daga karshe Allah ya hukunce ta da zuwa Amurka. A nan ne tayi karatun digiri ta na farko a fanni lisafi da fita da shigen kudi na kowane fanni a arayuwa (Bachalor of Science in Accounting). Bayan ta kammalla digirin ta, ba tare da hutawaba ta kara komawa makaranta domin neman digiri na biyu. A inda take karatun (Masters in Management Information System).

Tayi sha’awar zuwa karatu a kasar waje domin ta tashi a gidan su tare da iyaye ta da yayannin ta, ta fuskanci kowa yana kokarin yin karatu domin ya tsayu da kanshi. Iyayen ta basuyi karatu mai yawaba a rayuwar su, amma sun basu damar neman ilimi na addini da na boko. Yawan karance karance na littafan tafiyarda rayuwa da kuma jaridu tun tana karamarta ya budema ta idanu da cewar ‘ya mace zata iya neman ilimi a duk inda zata samu, kuma da cewar mace zata iya kawo ci gaba a rayuwarta, yaranta, mai gidanta, al’umarta, da jaharta idan tanada ilimi.