Wata mata ta fito da sanyin sassafiya tana gudun motsa jiki tare da Karen ta, sai suka ga wani kwali da alamun akwai wani abu mai motsi ciki. Sun isa don duba wannan kwalin sai suka ga wata karamar kyanwa a cikin kwalin.
Bude kwalin ke da wuya sai suka ga wata takarda da wani rubutu, koda ta duba rubutun sai ta ga rubutun dan-koyo, an rubuta dalilin da yasa aka yarda jaririyar magen. A rubutun ance “Saurayin mamata baya kaunata shiyasa zan rabu dake” Wannan rubutun na nuni da cewar duk wanda ya rubuta wannan sakon kuma ya ajiye magen nan yana kaunarta ne, baya sha’awar yadda ake muzguna ma kyanwar. Amma yin haka shine mafita ga kyanwar.
Kungiyar kare hakkin dabbobi sun dauki kyanwar kuma suna kara kira ga mutane su kokarta wajen mututunta rayuwar dabbobi. Domin suma suna da rai kamar kowa, babu dalilin da zai sa baza’a basu nasu hakkin ba a matsayin su na dabbobi.