Mawaki "50 Cent" Ya Fada Kwata

50 cent

Abun kamar magani ko tsafi! A duk lokacin da wani shahararen mawaki ko mawakiya ko dai wani fitattcce a wata sana’a suka yi kokarin sayar da wata kaddarar su sai aga sun shiga wani hali na ko yaya. Wani bincike da aka gudanar da ya bayyanar da cewar mafi yawan mutane da sukayi suna a duniya, sukan fuskanci matsalolin rashin kudi, bayan wasu shekaru. Hakan na kaisu ga siyar da kaddarorin su.

Sananen mawakin nan da aka fi sani da suna “50 Cent” ya mallaki wani katafaren gida, wanda ke da dakunkuna ashirin da daya 21, da bayi ashirin da biyar 25, a wata anguwa da ake kira “Poplar Hill Drive” ya saka wannan gidan a kasuwa don neman mai saye, akan kudi dallar Amurka miliyan takwas da dubu dari biyar $8.5 dai-dai da naira milliyan dubu dari da tamanin da bakwai 187,000,000 Tun a shekarar 2007 ya tallata gidan akan dala milliyan goma sha takwas da dari biyar. $18.5 amma ba a sayi gidan ba. Zuwa yanzu darajar gidan ta kara faduwa.

Tun bayan sayan gidan da yayi a shekara 2003 akan kudi dalar Amurka milliyan hudu da dubu dari daya $4.1 dai-dai da naira milliyan dubu dari tara da biyu 902,000,000, ya kuma kashe kimani milliyan shida zuwa goma $6 - $10 a cikin gidan, don dai gidan ya kai mishi yadda yake bukatar shi.