Rayuwar Karyace Ta Kare Ko Neman Asali Yasa Shi Tsiyacewa?

Tun a watan Satunba da mawakin nan “50 Cent” ya bayyanar da manufar shi ta zuwa kasashen Afrika don gano tushen shi, ake ganin ya shiga wani hali na rashin kudi. Shi ne dalilin da yasa ya saka gidan shi a kasuwa, abubuwa kuwa da ya saka a cikin gidan na alatu, sun hada da wajen motsa jiki na zamani, da wajen wasan ruwa da akafi sani da “Sweming pool” wajen wasan kwallon raga, da dai abubuwan shakatawa.

Rahoton na cewar alamu da suka nuna cewar duk fitaccen mutun da ya shiga sa’insa da hukumomi, to za’a ga cewar ya shiga wani hali, ko dai talauci ko waus masifu na rayuwa. Domin kuwa ai nihin gidan nashi, a hannun sannannen dan wasan boksin dinnan ne Mike Tyson, ya siya. A cewar wani dillali yana ganin kamar mawakin “50 Cent” daker ko zai iya samun milliyan biyar $5 dai-dai da naira milliyan dubu dari da goma 110,000,000 a kan gidan nashi.

Ana ganin dalilin da yasa gidan yaki sayuwa shine, irin makudan kudin da ake kashe ma gidan a kowane wata, kudin wuta, haraji, kudin ruwa, masu aiki da sauran su, da suka kai dallar Amurka dubu sittin da bakwai $67,000 dai-dai da naira milliyan gomasha hudu da dubu dari bakwai da arba’in 14,740,000. A zuwa yanzu dai ana bin mawakin kudi masu yawa, wanda suka hada da masu kudin lauyoyi, kudin gyaran kafet na gidan, wasu basusuka da ya dauka a wani kamfanin bada lamuni.