Dabbobi Ma Nada Hakkin Rayuwa Kamar Mutun

dog yawning

Wata kungiya masu rajin kare hakkin dabbobi a jihar New Hampshire, ta nan kasar Amurka, sun fitar da wata sanarwa cikin fushi cewar ya kamata a hana mutane amfani da bindiga wajen kashe dabbobi. Kimanin mutane sama da dubu talatin da shida 36,000 ne, suka saka hannu a takardar neman a canza wannan tsarin na kashe dabbobi ba tare da la’akari da suma suna da rai kamar kowa ba.

Hakan dai ya biyo bayan harbe wani Kare mai suna “Bruno” a lokacin dai da aka kashe Karen cikin halin muzgunawa, an harbe shi sau da yawa kamin ya mutu, a cewar Katie Treamer, wannan wani hali ne na rashin Imani da tausayi.

Babu dalilin da zaisa mutane su dinga kashe dabbobi, akan dalilin suna da wata cuta ko basa musu abubuwan, da suke bukata daga dabbobin. Don haka suna bukatar gwamnati su shigo cikin wannan maganar, a haramta kashe dabbobi, duk kuma wanda aka same shi yayi wannan aika-aikar, to ya kamata a hukunta shi matukar gaske.