Cigaba Na Kara Samuwa A Duniya: Kiran Acaba "Tasi" Da Wayar Salula

Acaba

Tafiya zuwa wajen aiki a cikin babban birnin Jakarta, na kasar Indonesia, kan iya zama wani babban abu, musamman idan akace da safiya lokacin zuwa wajen aiki da ‘yan makaranta ko dai-dai lokacin tasowa da aiki. Hanya mafi sauki don isa wajen da mutun ke da bukatar zuwa a wadannan lokuttan shine, mutun ya hau acaba “Babur”

Wasu matasa sun kirkiri wata hanya da mutane zasu iya kiran acaba ko mota “Tasi” a ko ina suke da wayar hannu. A kasashe da aka cigaba, ana amfani da irin wadannan tsarin ne wajen kiran motar haya, amma su a kasar Indonesi a karon farko sun kirkiri wanda har mashin ma ana iya kiran shi ta amfani da wayar hannu.

Wani babban abun sha’awa da wannan kamfanin mai suna “Ladyjek” suna da mashina na kabo-kabo, da suke ba ma'aikatan su, amma mata kawai suke dauka aiki, wanda mata ne ke sana’ar acaba, kuma a duk lokacin da mutun ke bukatar dan’acaba ya zo kofar gida ya dauke shi, kawai sai yayi amfani da wayar hannu, nan-da-nan duk wata mace dake kusa da gidan mutun, da ke sana’ar acaba zata zo kofar gida ta dauki mutun. Suna da wata kararrawa da zata gaya ma mutun ana da bukatar acaba a waje kaza.