Wasu Daga Cikin Tsofaffin Shugabannin Amurka Da Kudin Su

Shugaban Amurka Da suka fi kusi

A cigaba da kawo muku adadin abun da tsofaffin shugabannin kasar Amurka, suka mallaka a lokacin rayuwar su, zamu daura akan shugaban kasa "Lyndon B. Johnson" wanda shine na bakwai 7. Ya zamo shugaban kasa ne bayan kashe shugaban kasa JF Kennedy, a wancan lokacin, a lokacin mulkin shi yayi yaki da talauci, shima dai mafi akasarin kudin shi sun zone daga sana’ar filaye da ya keyi a jihar Texas, jihar da tafi kowacce girma a baki daya kasar. Yana da dallar Amurka $98M dai-dai da naira =N=21,560,000,000

Haka shugaban kasa “Herbert Hoover” shine yazo na takwas 8, nashi kudin ya banbanta da sauran, domin shi bai gaji kudi ba. Shi maraya ne bai san iyayen shi ba, amma ya samu kudin shi ne a sana’ar hako ma’adanan kasa. Yana da dallar Amurka $75M dai-dai da naira =N=16,500,000,000.

Na tara kuwa a kudi shine “Franklin D. Roosevelt” shine shugaban kasar Amurka, da yafi kowannen dadewa a karagar mulki, yayi mulki na fiye da shekaru goma sha biyu 12. Ya dai gaji wasu kudi a wajen mahaifin shi da kuma matar shi Eleanor, Yana da dallar Amurka $60M dai-dai da naira =N=13,200,000,000.