Yawanci mutane sunfi jin ance gasar wanda sukafi kyau, kokari, baiwa, da dai makamantan hakan. Amma a kasar Zimbabwe, akanyi gasar marasa kyau a kasar. Maison Sere, mai shekaru arba’in da biyu 42, shine ya lashe gasar wannan shekarar, a matsayin mutun da yafi kowa rashin kyau, muni a daukacin kasar.
Ya samu kyautar kudi na dallar Amurka dari biyar $500 dai-dai da naira dubu dari da ashirin 120,000. Kasar tana fama da rashin aikinyi ga matasa, haka kuma tattalin arzikin kasar yana cikin wani hali, wanda yasa kyautar $500, ta iya zama wata abu da kowa na iya shiga gasar idan yana da yakinin lashe gasar.
An dai tashi a gasar cikin rudani, inda Mr. William Masvinu, yake zargin alkalan gasar da sonkai, domin yana ganin shine ya lashe gasar, domin kuwa a shekaru uku 3, da aka fara wannan gasar shike zuwa na daya, amma sai gashi yazo na biyu wanda aka bashi kyautar dalla dari daya $100 dai-dai da naira dubu ashirin da biyar 25,000. Ya bukaci da a sake alkalan gasar kuma a sake gasar domin kuwa idan akayi haka zai lashe gasar.
A tabakin Mr. David Machowa, wanda ya kirkiri wannan gasar a shekarar 2012, yace ya kirkiri wannan gasar ne don, "bayyanar da kyau a cikin muni" Ya kara da cewar yanzu ma haka yana shirin gudanar da gasar munana ta duniya.