Matasa Kunyi Tsare-Tsare Da Fatar Alkhairi Ga Sabuwar Shekara?

Ganin cewar karshen shekara na kara matsowa, kuma bukukuwa a karshen shekara wani abu ne da yake zuwa duk bayan shekara. A haka yakamata matasa su kokarta kyautata zumunta da kawance a tsakanin abokai da dangi.

Abubuwa sun zo da sauki a wannan lokaci da ake ciki, ganin cewar mutun na iya yin amfani da shafufukan shin na yanar gizo, wajen bayyana ma ‘yan-uwa da abokana arziki irin halin da yake ciki. Musamman yadda yake gudanar da shagulgulan bukukuwan karshen shekara da bukin “Chrimas” Lokacin bukukuwa ba lokuttan batama juna rai bane, lokacine na murna da annashuwa, haka mutane suyi amfani da damar neman gafara ga juna haka da tsarama kansu wasu abubuwa da suke son cinma buri a sabuwar shekara.

Masana na kara jawo hankalin matasa da suyi taka tsan-tsan wajen irin abubuwa da zasu saka a shafufukan su, domin wasu na iya amfani da wannan lokacin wajen yimu su wasu munanan abubuwa. Matasa kada su dinga nuna irin wajajen da suke a lokacin da suke, don hakan na iya bama miyagu damar shiga gidaje dakunkuna don dauke-dauke, idan suka tabbatar da mutane basa kusa.