Shugaban Facebook Zai Dauki Hutun Wata 2 Don Sabuwar Jaririya

Shugaban kamfanin acebook Mark Zuckerberg

Shugaban kamfanin shafin zumunta na “Facebook” Mark Zuckerberg, ya bayyanar da cewar zai dauki hutun wata biyu, don ya zauna da matar shi, a dai-dai lokacin da suke tsammani zata haifi ‘ya-mace. Yace dama akan tsarin da dokoki na kamfanin, duk wanda yake da mata ko mace suna da damar daukar hutun wata hudu, idan aka samu karuwa a tsakanin ma’aikaci ko ma’aikaciya.

Kuma ma’aikata nada damar daukar wannan hutun a lokaci daya, ko kuma su raba shi a duk lokacin da suke so, a cikin shekarar farko da haihuwar jaririn. Yace ko kuma wanda bashi da bukatar haka ana iya biyan shi kudin hutun sai ya zauna yayi aiki.

Kamfanin shine dai wanda yafi kowanne kamfani girma a duniya, a bangaren zumunta na yanar gizo. Har ya zuwa yanzu shugaban Mark, bai bayyanar da wa zai dauki ragamar kamfanin ba idan baya nan. Amma amfi tunanin Sharyl Sandberg, shugaban gudanarwa na kamfanin shi zai rike shugabancin kamfanin na wucin gadi.