Wani kamfanin kasar Ingila, da kanyi ma makarantu rubutun wata takarda da akan bama yara wadannda sukayi kokari a aji wato “Sticker” a turance. A irin tsarin makarantu a kasar, malamai sukan bama dalibai wannan stikar idan yaro yayi kokari a aji, ko kuma ya zama mai biyayya ga malamai.
Idan kuma yaro ya zamana baya jin magana, akan bashi stika wadda take dauke da hoton wani abu mara kyau, hakan ya kansa yara su maida hankali don kada a basu irin wannan takardar. A wani bincike da kamfanin ya gudanar yace, ya gano cewar akwai wasu sunannaki da idan aka sama yaro ko yarinya, sukan zama masu ladabi da biyyaya, amma idan aka sama yaro ko yarinya wasu sunanana ki, sukan zama marasa jin magana.
Dalilin su kuwa shine, cikin jerin yara dubu saba'in 70,000 da aka bama stika ta kyautata abubuwa da masu munanan abubuwa. Yara da suke da suna a bangaren mata Anna, Courtney, Millie da Mia, akwai alamun yara ne masu kokari haukuri da hazaka. Haka ma a bangaren maza idan yaro yana da sunan Harry, Ryan, Ethan, da Lewis.
Amma idan akace yarinya tana da sunan Leah, Eleanor, da Abifail, to a guji mai irin wannan suanan. Sai ta bangaren maza, masu suna Joseph, James, da Joshua, wadannan sunanankin kan iya sa wadannan rayan rashin jin magana. A karshe dai sunce ba wai dole hakan ya kasance gaskiya ba. Amma da a'akwai alamun hakan na iya zama gaskia da kashi 70%.
Don haka a naku yankin wadanne sunanaki ne kuke ganin idan yara suna da su basu jin magana? Ku rubuto muna a shafin mu na dandalinvoa/facebook.com