Masana kimiyyar binciken arzikin kasa wato “Anthropologies” a kasar Masar “Egypt” sun bayyanar da cewar suna da yakini kashi casa’in 90% cewar suna kara gano wasu dakun-kuna na sarauniya Nefertiti, wadda tayi zamani kimanin shekaru dubu uku da dari uku 3,300 da suka wuce.
A dai-dai wajen da mutun-mutumin wani sarki Tutankhamun, yake sun gano cewar kar-kashin kasan shi wani daki ne wanda ke dauke da wasu dukiyoyi, da ba’a taba sanin dasu ba, amma yanzu suna kara bincike don ganin sun shiga ciki da kyamarori don daukar hoton dakin dake cikin kasa.
An dai fara wannan binciken ne cikin kwanaki uku da suka wuce, a birnin Luxor, a cewar ministan albarkatun kasa Mahdouh el-Damaty, duk abun da aka samo za’a kaisu kasar Japan don amfani da wasu na’u’rori wajen bayyanar da yawan shekarun su, kamin a cigaba da tono wadannan abubuwan tarihin. Shi dai garin na Luxor, damar gari ne da ke da dunbin tarihi, domin kuwa ansamu abubuwan mutane da masu yawa a garin. Kuma gari ne da yafi yawan mutun-mutumin mutanen da.