A Haduwar Farko Macce Na Iya Gane Cewar Saurayi Ya Mutu A Kanta

Samartaka

‘Yan-mata sun san ta yadda suke kama samari, mata ne kawai keda basirar gane idan saurayi ya mutu a kan mace, wanda daga nan sai a fara ja mishi aji. A tabakin wani manazarcin halayyan matasa Dr. Paul Dobransky. Yace akwai wasu abubuwa guda 8, da matasa kanyi da yake bama 'yan-mata karfin gwiwar cewar saurayi na sonta.

Na farko shine, a duk lokacin da samari suka ga mace, abun da suke fara kallo shine ya surar jikin ta yake, tana da jiki ko kuwa bata da jiki, haka kuma ya take tafiya? ta kanyi tafiya kamar ‘yar zamani. Sukan kuma lura da ya take dariya da murmushi. Haka sau da dama samari sukan so su ga mace tana da gashi, koda kuwa ba nata bane. Babu ma kamar ace yarinyar matashi yace mai kananan shekaru.

Haka matasa kan mutu a kan mace da ta iya kwalliya, da ta iya shafa jan-baki, gazar, hoda, da ma saka kaya masu tsukewa. Sau da yawa samari sukan lura da wace irin jaka budurwa take rike da ita, duk wadannan abubuwan sukan sa ‘yan mata su gane idan namiji ya mutu a kansu a hadduwar farko. Daga mace ta iya gane cewar saurayi ya lura da duk wadannan abubuwan a kanta, a dai-dai wannan lokacin ne ita kuma zata fara nata lokacin na yanga. A takaice dai ana iya cewar mata sunfi samari wayo ke nan?