Gidaje Da Sukafi Tsada A Shekarar 2015

Shakira's Mansion

Kowace shekara takanzo da irin nata tarihin, haka kuma a karshen kowace shekara ana iya duba wasu abubuwa da suka faru a shekarar kodai suna kama da shekarar da ta gabata ko kuwa sun banbanta a wurare da dama.

Shekarar 2015 ba’a barta a bayaba, domin kuwa abubuwa da dama sun faru, wanda baza a manta da suba. Shekarar 2015 nata salon shine yadda tsarin gidaje ya dauki wani salo, domin kuwa a shekarun da suka gabata yadda ake tsarin gidajen masarauta ya banbanta da yadda na sauran al’umah suke, daga wajen girma zuwa kalolin fainti, zane-zanen kayatarwa da dai makamantan su. A wannan shekarar ta 2015 an sayar da wasu gidaje da su kafi tsada da kayatarwa a nan kasar Amurka.

Gidan farko an siyar da shine akan kudi dallar Amurka milliyan $46.3M kwatankwacin naira billiyan 9,200,000,000, wanda yake mallakar wani fitaccen mawakin Kaboyi da ake cewa (Country music) Kenny Rogers. Gidan dai na jihar California a birnin Los Angeles.

Sai na biyu an siyar da shine akan kudi dallar Amurka milliyan $33M kwatankwacin naira billiyan 6,600,000,000, wanda yake mallakar fitacciyar mawakiyar nan Jennifer Lopez, a da. Gidan na bakin gabar tekun Miami, a jihar Florida.

Gidan na uku kuwa an siyar da shine akan kudi dallar Amurka milliyan $31M kwatankwacin naira billiyan 6,200,000,000, wanda aka ginashi tun a shekarar 1910, amma yasha kwaskwarima da yayi dai-dai da zamani, yana yankin San Francisco.

Na hudu kuwa an siyar da shi ne akan kudi dallar Amurka, milliyan $27.5M kwatankwacin naira billiyan 5,500,000,000, yana kuma anguwar Bridgehampton, jihar New York.

Na biyar kuwa an siyar da shi ne akan kudi dallar Amurka milliyan $23M kwatankwacin naira billiyan 4,600,000,000 yana yankin Santa Monica, a jihar California.