Garuruwa Da Kanfi Samun Yawan Dusar Kankara A Kasar Amurka!

Garin Johnson City, a jihar New York na daya daga cikin jerin garuruwan da sukafi samun matsananciyar dusar kankara a kasar Amurka, sukan samu dusar kankara da takai kimanin inci 83.4, a shekara, sai garin Alpena, a jihar Michigan, da kan sami kimanin inci 84.3, haka garin Benton Harbor, duk a jihar ta Michigan, sukan samu kimanin inci 84.5 a shekara.

A cikin jerin garuruwan kuwa sun hada da garin Dulth, a jihar Minnesota, da suke samun kimanin inci 86.1, sai garin Juneau, a jihar Arkinsa, da kan damu inci 86.7, suma a cikin shekara, haka garin Boulder, a jihar Colorado, sukan samu kimanin inci 88.3 cikin shekara, haka suma garin Cortland, a jihar New York na biye da kimanin inci 90.3 a shekara, sai garin Bozeman, a jihar Massachusetts, da sukan samu kimanin inci 91.0, suma garin na Muskeng, a jihar Michigan na biye da su a wajen samun dusar kankara mai matsanancin yawa da ta kai kimanin inci 93.7.

Manya kuwa sune garin Buffalo, a jihar ta New York da sukan samu kimanin inci 94.7 a shekara, haka ma garin Salt Lake City, da ke jihar Uta, sukan samu kimanin inci 95.1 haka ma garin Colorado Sprongs, a jihar Colorado, sukan samu matsananciyar dusar kankara da takai inci 95.4. Garin Jamestown, na biye da sauran garuruwan da kimanin inci 97.5. Wato abun duwaba a nan shine. Za’a ga cewar wasu garuruwan suna yankin arewa, wasu kuma suna tsakiya amma sai gashi sukan samu dusar kankara, fiye ma da wasu garuruwan da ke arewacin kasar. Mafi akasari amfi tsanmanin dusar kankarar a jihohin yankin arewa.