Damisa Tayi Wasan Kura A Cikin Wata Makaranta A Kasar India

Tiger iran

A ranar Lahadi da ta gabata ne, wata damisa ta shiga wata makaranta mai suna “Vibgyor International School” a garin Bangalore kasar India. Damisar dai tayi ma mutane shida rauni, a lokacin da suke kokarin kamata. Duk dai da cewar raunin da ta jimusu ba wai munmunan rauni bane.

An kwashe sama da awowi goma 10, ana kokarin kama wannan damisar, har sai da ta kai an harbeta da wasu allurai da suka kashe mata karfin jiki. Cikin wadanda tajima rauni sun hada da wani masani a harkar kimiyya da fasaha, haka kuma da ma’aikacin gandun daji, sai mai aikin daukar bidiyon yadda abubuwan keta gudana.