Garuruwa Da Su Kafi Samun Baki A Fadin Duniya

Wani kamfani mai suna “Euromonitor International” sun fitar da wata kididdiga da suka bayyanar da garuruwa a wasu kasashe a duniya da sukafi samun baki ‘yan yawon ganin gari. Sunyi amfani da wasu alkalumma wajen gano wane gari ne a fadin duniya, baki su kafi kwarara a cikin shekara, duk a fadin duniya.

A cewar su, kasashen yankin Asia, suke da kaso mai yawa na samun baki a cikin shekara, sai kasar Amurka da kasashen Turai, haka da kasashen Larabawa. Sun kuma fitar da kasashen da garuruwa da adadin yawan mutane da suka ziyarta a cikin shekarar da ta gabata. Garin Hong Kong, na kasar China, shine gari na farko da yafi samun baki ‘yan yawaon shakatawa da suka haura mutane milliyan 27.8, a shekara, sai kasar Ingila da ke samun mutane milliyan 17.4, sai kasar Singapore da mutane milliyan 17.1 duk a shekara.

Garin Bangkok, kuwa na kasar Thailand, nada milliyan 16.2, sai kasar Paris, da ta samu milliyan 14.97, haka garin Macau, a kasar China, sun samu mutane milliyan 14.96, kana garin Shenzhen, duk a kasar China, sun samu mutane milliyan 13.1 cikin shekarar da ta gabata.