Shafufukan Zumunta Kan Iya Kai Mutun Ko'ina A Rayuwa

Ta wadannen irin hanyoyi ya kamata mutane suyi amfani da shafufukan su na zumunta kamar su facebook, twitter, don kasuwanci? Shahararen mawakin nan na kasar Amurka, Kanye West, yayi amfani da wannan damar wajen ganin yayi kasuwanci da yake sa ran zai kai shi ga tudun tsira.

Shi dai mawakin dan asalin garin Chicago, ya rubuta a shafin shi na twitter, cewar banki na binshi bashi da ya kai kimanin dallar Amurka milliyan $53M wanda hakan ya kawo tsaiko gare shi da cigaba da kasuwancin nashi na waka. Amma ya rubuta a shafin shugaban kamfanin shafin zumunta na Facebook Mr. Mark Zuckerberg, da cewar yazo ya saka hannun jari na dallar Amurka $1B billiyan daya a harkar tashi ta waka, don ya samu ya mike. Mr. Mark, ya zubuta mishi cewar na saka hannun jari? Nasan wannan harkar taka ce, amma kana iya kirana gobe sai mu tattauna.

Mawakin ya sake rubuta mishi da cewar, gaskiya ina bukatar taimakon ka shi yasa nafito bayyanar jama’a domin so nake ka taimaka kasaka hannun jari a wannan sana’ar tawa. Wannan kadan daga cikin irin yadda mutane zasu iya amfani da shafufukan su na zumunta wajen tallata hajar su da kuma samun karbuwa a duniya.