Mai Kamfanin Facebook Ya Shiga Jerin Masu Kudin Duniya 2016!

Mark Zuckerberg

A cikin jerin masu kudin duniya na shekarar 2016, wanda ya zama na shida kuwa shine Mark Zuckerberg, mai shekaru 31, da haihuwa, shi ke da kamfanin sada zumunta na facebook, matashi a cikin jerin manya masu kudi na duniya, yana da kimanin dallar Amurka billiyan $44.6B. Haka na bakwai kuwa Larry Ellison, mai shekaru 71 a duniya, shi ke da kamfanin “Oracle” kamfanin da ke kera wasu daga cikin bangarorin kwamfuta da suka hada da na bayyane da na boye. Yana da adadin kimanin dallar Amurka billiyan $43.6B.

Na takwas kuwa shine Machael Bloomberg, mai shekaru 74 a duniya, kamfanin shi ya shahara wajen aikin jarida na gidan talabijin, yana da kimanin dallar Amurka billiyan $40B. Haka na Tara kuwa shine Charles Koch, mai shekaru 80 da haihuwa, cikakken dan kasuwa ne da ya shiga kasuwanci da dama. Ya mallaki kimanin dallar Amurka billiyan $39.6B.

A wannan shekarar an samu wanda su kayi kunnen doki a mataki na tara, David Koch, shima ya mallaki adadin kudi kimanin dallar Amurka billiyan $39.6B. Yana da shekaru 75 a duniya. Shima yana kasuwanci da dama. A karon farko dai Zuckerberg da Bezos, sun shiga cikin jerin masu kudin duniya.