'Yan-Mata Hattara Dai! Kada Garin Neman Kiba A Samo Rama

Hattara dai ‘yan-mata! Kada garin neman kiba a kwaso rama. Wannan wani gargadi ne da taron kwararru masana a harkar kiwon lafiyar fata su kayi. An kaddamar da kasidu da dama dangane da wasu cututtuka da kan haifar da matsaloli ga fatar dan’adam, da kan iya zama cutar da zata shiga cikin jiki.

A wani bincike da suka gudanar da ya nuna cewar wasu abubuwa da ‘yan-mata kan dauka cewar basu da wata matsala ga fatar su, sau da yawa su kanyi amfani da buroshi da suke shafe-shafe a fuskokin su a kowane lokaci. An iya gane cewar wannan buroshin kan dauko wasu kwayoyin cututtuka kuma su kanyi amfani da buroshi daya don shafe-shafe na tsawon lokaci wanda ta nan ne cuttutuka ke shiga.

Haka ‘yan-mata da yawa kanyi amfani da buroshi da ke dauke da wani nau’I na mai da kan iya cutar da fata suyi amfani da shi wajen shafe-shafe, kuma su kanyi amfani da tsunman da suke goge kwalliyar su batare da wankewa ba ko sake wani mara wasu abubuwa.

Yawan amfani da abun shafe-shafe daya ko kuma rashin canza kayan kwalliya kan iya zama illa ga hallitun da ke kare fata. A cewar Dr. Engelman, idan mata basu kiyaye ba wajen amfani da abubuwan da suka dace da fatar suba, hakan zai haifar da abubuwa da dama, kamar su jemewar fata da wuri, mace ta koma kamar tsohuwa haka da kamuwa da wata cuta da kan shafi karfin ido. Don haka akwai bukatar mata su kiyaye abubuwan da suke saka ma fatar su da kuma neman shawara daga masana kiwon lafiyar fata.