Shugaban kasar Amurka, Barak Obama, a karon farko ya ziyarci kasar Cuba, jiya Lahadi, inda ake sa ran zai kwashe tsawon kwanaki 3 a kasar, bayan wata daddadiyar gaba ta tsawon shekaru 88, a tsakanin kasashen biyu. Kasar Amurka da Cuba, sun shiga takun saka tsakanin su, wanda hakan ya haifar da rashin jituwa a tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Obama, shine zababben shugaban kasar Amurka, da ya ziyarci kasar a matsayin mai bukatar dangantaka a tsakanin kasashen biyu ta dawo kamar da. Shugaba Obama, dai ya isa babban birnin kasar inda uwargidan shi Michelle Obama da ‘yayan shi biyu Sasha da Malia, suka raka shi.
Shugaban Obama dai zai gana da shugaban kasar ta Cuba, Raul Castro, wanda ya gaji wanshi a karagar mulki, kuma wanshi Fidal Castro, shine shugaba da ya jagoranci fada a tsakanin kasashen biyu, shekaru da dama da suka wuce. Shugaba Obama zai kuma yawata a cikin kasar don kokarin gyara dangantaka a tsakanin kasashen biyu, amma ba zai samu ganawa da tsohon shuagabana kasar ba Fidal Castro.