Wasu Yankuna Da Komi Girman Mutun A Duniya Baya Iya Zuwa

Bincike ya bayyanar da wasu gurare a fadin duniya da babu mahaluki da kan shiga yanku nan, wasu daga cikin guraren sun hada da kamar gidaje, wasu dazuzuka, ko wasu yanki da gwamnatoci a kasashe daban-daban basu bari mutane su kai wajen don wasu dalilai na daban.

Komi girman mutun a duniya akwai wuraren da mukamin shi ba zai taba kai shi ba. A kasar Norway, akai wani runbun ajiyar irin kowane kalan abunci a duniya da ake ajiyar shi a wani gida, ana kiran gidan “Svalbard Global Seed Vault” wannan gidan yana cikin wani kungurmin daji da babu mutun sai namun daji, akwai iri na kowane irin nau’in abucin da suka kai sama da nau'i milliyan dari biyu da hamsin, a fadin duniya akwai shi a wajen. Wadanda kawai ke iya zuwa wajen sai manya-manyan masu bincike na duniya, wanda a tarihi har zuwa yau ba’a samu mutane da suka wuce 5 da suka taba shiga gidan ba.

Sai wani yanki a jihar Navada da ake kira “Area 51” babu wani mutun dake ziyartar wannan dajin, wannan wani sansanin sojojin kasar Amurka ne, akwai wasu abubuwan sirri na kasar ta Amurka da ba’a bar kowa yaje wajen. Haka wani daki da ake ajiye takardun sirri na mabiya addinin kiristanci a kasar Rome, fadar shugaba Fafaroma ta “Vatican” akwai wasu takardun sirri da ba kowa ke iya ganin suba. Haka ma a kasar Ingila, akwai wani sansanin ajiyar kayan sirri na yaki na sojojin kasar ta Ingila da babu wanda ke iya zuwa wajen da ake kira “Raf Menwith Hill”