Masana Sun Gano Karin Muhinmancin Ruwa A Jikin Dan'Adam

water

Da akwai bukatar adadin yawan ruwa da ake so kowanne mutun ya sha a rana. Masana sun gudanar da bincike da dama da ya nuna cewar, kwakwalwar mutun na da bukatar adadin yawan ruwa a rana don samun gudanar da aiki yadda ya kamata.

A cewar wani babban likita Dr. Robert A. Huggins, na asibitin koyarwa a jami’ar Connecticut, ta kasar Amurka, yace kwakwalwar mutun na bukatar akalla yawan ruwa da suka kai “8*8” wanda yayi dai-dai da yawan ledar fiyowata 5 a rana. Ya kara da cewar kwakwalwar mutun na da nauyin kashi 3.5% na nauyin mutun, amma ita ke cin fiye da kashi 20% na duk wani abu da mutun ya keci, hakan na nuna cewar kwakwalwa tafi kaso maiyawa da sauran sassan jikin mutun.

Hakan yasa tana bukatar ruwa masu tsafta da yawa don gudanar da aiki yadda ya kamata a cikin lokaci. Sai ya kara da cewar hakama idan jiki na lafiya akwai bukatar motsa jikin, don ta hakan kwakwalwar ke kara samun kuzari da aiki yadda yakamata. Domin kuwa idan jini ya isa cikin kwakwalwa zai bukaci yawo a bangarori daban-daban na kwakwalwar. Wannan binciken ya kara tabbatar da muhimancin ruwa a cikin jikin mutun a kowane lokaci.