Dalilan Dake Sa Warin Baki Ga Samari Da 'Yan-Mata!

teeth whitining

Wasu dalilai da dama da kan sa mutun warin baki, idan har mutun zai ci abinci batare da ya wanke bakin shi ba, haka kuma da wanke halce akai akai, to wadannan dabi’un sukan haddasa ma mutun warin baki. Likitoci sun bayyanar da wasu hanyoyi da mutun zai bi don gujema warin baki da kuma kokarin samun inaganatacciyar lafiya ga mutun.

Akwai bukatar a duk lokaci da mutun ya gama cin abinci ya kokarta wanke bakin shi, ya kuma yi sakace tsakanin hakoranshi don fitar da duk wani abinci da ya rage a tsakani. Haka kuma idan mutun yana jin miyau a bakin shi yana bushewa to ya hanzarta shan ruwa domin wannan alamu ne na kishi. Rashin wadataccen ruwa a jikin mutun shima yakan haddasa warin baki.

A duk lokacin da bakin mutun ya bushe kuma yana da ragowar abinci a bakin shi, to a dai-dai wannan lokacin ne wasu hallitu da ake kira “bacteria” a turance, ke saka cuta a bakin mutun, su kan bayyana a cikin baki sai su saka ma mutun warin bari a dalilin suna cin abincin da ya rage. Idan aka dace da mutun bai wanke bakin shi, cikin-cikin shi zai dinga wari kasancewar babu ruwa dake gudana a cikin jikin shi. Hakan kansa samari ko 'yan mata rasa abokan soyayya, don haka zai a kula kuma a kiyaye.