An kaddamar da wani rahoton bincike da aka gudanar, rahoton nada ban mamaki. Wasu jerin masana a kasar Brazil, sun gudanar da wani bincike akan wasu dalilai da suke haifar da wasu cuttutuka da akan sha wuya wajen gano su, hasali ma su kanyi sanadiyar mutuwa.
A rahoton sun bayyanar da cewar yawan zama na haddasa abubuwa da dama a jikin dan’adam, da kawo mutuwa kusa. A bincike da suka gudanar a kasashe hamsin da hudu, wanda suka nuna cewar idan mutane suna zama a waje daya na fiye da tsawon awowi hudu batare da tashi suna kai komo ba, to wannan dadewa suna zaune kan haifar musu da cuttuka da dama.
Sun kara da cewar koda kuwa mutun ya kanyi atisaye akai akai, idan dai yana zama fiye da awowi hudu a lokaci daya, to wannan atisayen bazai iya maye gurbin zama da mutun yayi na tsawon lokaci ba, domin kuwa cutar tayi nisa a cikin jikin da ba karamin abune zai iya shawo kanta ba.
Suna ganin cewar, zama mafi tsawo da ya kamata mutun yayi a rana shine na tsawon kasa da awowi ukku. Sun bayyanar da cewar mutane su kokarta wajen ganin sun takaita zaman su a rana, su yawaita tsayuwa da juya jikin su koda kuwa suna zaune da tsaye ne, don hakan zai taimaka ma gabobi da jini samun gudana yadda ya kamata.