A karon farko, wasu matuka jirgin sama ‘yan kasar “Switzerland” su biyu sun tuka jirgin saman farko dake aiki ba tare da ruwan mai ba, shi dai jirgin yana amfani da hasken rana wajen samun karfin tashi da tafiya a cikin sararin samaniya.
Jirgin shine na farko a duniya da aka fara kerawa wanda yake da injina hudu, da suke samun wuta daga injin da aka gina mai daukar wuta daga hasken rana. Matukin jirgin Mr. Bertrand Piccard, ya sadaukar da rayuwar shi, inda yayi yawo a cikin jirgin na tsawon kwanki uku a yankin Tekun “Pacific” yace a tsawon kwanaki ukun, ya kanyi baccin kimanin mintoci ashiri ne kawai a rana.
Yayi ta kokarin magana da masu kula da shawagin jirage na kasashen Turai, kasancewar cikin jirgin babu na’urar dumama daki ko ta sanyayawa. Yace duk dai da cewar wannan shine jirgi na farko a duniya da baya aiki da mai, to shi wannan wani abun jin dadi ne gare shi na fara tuka irin jirgin.