Leicester City Ta Lashe A Karon Farko A Shekaru 132

Leicester City

Kungiyar Kwallon kafa ta Leicester city, ta lashe gasar frimiya lig na bana sakamakon wasan da aka yi tsakanin Chelsea da Tottenham jiya dama ita Tottenham, tana bukatar samun nasara a duk wasanin da zata buga ita kuma Chelea ta samu nakasu koda a wasa guda daya, sai ya kasance an tashi wasan biyu da biyu.

Wannan shi ya baiwa Leicester nasara wanda yake koda ta barar da wasanin ta biyu da suka rage kofin nata ne.

Wannan shine karon farko da kungiyar tayi nasarar cin wannan kofi tun kafa kungiyar shekaru dari da talatin da uku kennan, kuma kudin da aka saye ‘yan kwallo biyu a manyan kungiyoyi kamar Manchester United ko Barcelona, zai saye ‘yan kwallon Leicester goma sha daya.

Wannan nasara da Leicester City ta samu ya bata damar fitowa cikin manyan kungiyoyin wasan kwallo na duniya.

Yanzu dambarwar ta rage tsakanin Tottenham, Arsenal, Manchester da Manchester City, bukatar Manchester United shine a doke Manchester City, ita kuma ta lsashe wasanin ta domin ta samu damar buga kofin kwararru na nahiyar Turai a shekara mai zuwa.