Dubun Wani Sojan Gona Ta Cika Yanzu Yana Hannu

Dubun wani Sojan gona mai suna George Edem, ta cika, shi dai wannan Sojan gona an kama shine a lokacin da ya je wajen hukuma domin karbo wa wani Babur din sa na hawa.

Bayan da ya shiga hannun hukuma Edem, ya amsa laifuffuka da ya aikata da suka hada damfarar mutane da kuma yin zamba.

Ya kuma kara da cewa ya yaudari jami’an ‘yan Sanda da dama inda yake nuna masu cewa shi Soja ne kuma yake amfani da wanna dama domin shiga tsakani ‘yan Sanda da wadanda ake tuhuma da laifuffuka.

Edem, ya kwashe shakaru takwas yana wannan aika aika, ya kuma ce ya karbi kudade da dama a hannun mutanen dake da matsala da kwastam ko ‘yan Sanda da zammar cewa zai sama masu mashala.