An Damke Wata Mata Mai Satar Yara

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta kama wata mata mai suna Maryam Mohammed, wanda ake zargi da satar wata yarinya Azizah Shitu, ‘yar shekaru takwas da haifu.

Maryam, ‘yar shekaru ashirin da biyu da haihuwa an kama ta ne a lokacin da take kokarin guduwa da yariyar da ta sata daga unguwar Gabi, a garin Soro, dake cikin jihar Bauchi.

Dan Sandan ciki na gundumar Soro, Mohammad, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, cewa an damke ta ne a Kamfanin kutare ne a akan hanyar Bauchi zuwa Maiduguri, a lokacin da take kokarin shiga mota da yariya zuwa inda ba’a sani ba.

Ita dai wannan yarinya Azizah Shitu, tun 4, ga watan nan ne dai ke ta nemanta, ya kara da cewa bincike ya nuna cewa wannan ba shine laifin Maryam na farko ba.