Dan Shekaru 16, Ya Tabbatar Da Kananan Shekaru Sune Lokacin Zama Billoniya!

Matashi Ben Pasternak

Yawan shekaru ba sune hankali ba, ko kuma arzikin mutun. Kowa ne dan’adam da yadda Allah, ya tsara mishi rayuwar shi, da yadda arzikin shi zaizo har iya karshen rayuwar shi. Yawaita tunani, hangen nesa, da duba rayuwar wasu da suka cigaba, a tsakanin matasa wani abu ne da kan kara ma matasa gwarin gwiwa don kokarin zama wani abu a rayuwa. Idan akayi la’akari da rayuwar Ben Pasternak, mai shekaru goma shashida 16, da haihuwa.

Wanda ya zama shugaban wani kamfani mai makudan milliyoyi jari. Shi dai Ben, ya kirkiri wata manhaja, wanda matasa kanyi amfani da ita wajen saye da siyarwar da wasu abubuwa, da suke da su ko su kayi amfani da su, amma basu da sauran bukatar su. Matasa kanyi amfani da wannan manhajar mai suna “Flogg” inda suke bukatar amfani da wayar hannu, su dauki hoton abun da suke da shi don siyarwa ga mabukata.

Idan har mutun na da bukatar siyan wani abu da ya gani a shafin Flogg, sai suyi mahada suba shi kayan ya biya su kudi. Yanzu haka dai manya-manyan kamfanoni da sukayi fice a harkar kimmiya da fasaha a duniya, suna kokarin sa hannun jari a kamfanin wannan matasahin don taimaka mishi.