Ashe Warin Baki Na Lalata Soyayya, Tsakanin Saurayi Da Budurwa?

49ers Broncos Football

Kadan daga cikin mutane ne suka san muhimancin wanke baki, sau biyu ko uku a rana. Babu wata hanya da mutun zai bayyanar da matukar muhimancin wanke baki akai-akai. Da ya wuce tabbatar da samun inagantacciyar lafiya, da kyautata dangantaka tsakanin masoya.

Wani bincike da aka gudanar, ya bayyanar da cewar, ‘yan mata sukan kara son samarin su, idan sun kasance suna da tsafta, musamman tsaftar baki. A duk lokacin da yarinya ta fuskanci saurayi nada warin baki ko baya wanke bakin shi akai-akai, to ‘yan mata kan ja baya akan wannan saurayin. Dr. Jonathan Abenaim, na jami'ar jihar New York, a nan kasar Amurka ya bayyanar da sakamakon wannan binciken.

Kimanin ‘yan mata sama da dari 100, da aka gudanar da wani bincike da su shiga. Kashi arba’in da biyu 42%, sun bayyanar da cewar sun rabu da samarin su ne, a dalilin warin baki da samarin suke da. Ba wai don irin kazantar su ta jiki ba, sunce da dama daga cikin samarin basa goge bakin su kamar yadda ya kamata, domi kuwa suna ganin hakoran su sunayin wani kala na daban. An alakanta yawan ciye-ciye batare da wanke baki akai-akai ba, a matsayin abun da kan haifar da warin baki a tsakanin samari da 'yan mata.