Matakan Farko Don Kaurace Ma Ciwon Asma!

Sakamakon wani bincike da aka fitar, na nuni da cewar sama da kashi saba’in 70% na mutane dake dauke da ciwon Asma, suna dauke da wasu kananan cututtuka. Hakan na bayyanar da matukar muhimancin daukar wasu matakai don kare kai daga wadannan kananan cututtukan.

Haka wadanda suka gudanar da binciken, sun bayyanar da wasu abubuwa guda goma da ya kamata, mutane su sani akan wannan ciwon. Na daya ita dai cutar ba kawai ta tsaya ga yawan tsinkewar nunfashi bane, shi yasa shan maganin da aka rubuta, koda ciwon bai taso ba yake da muhimanci. Ciwon ba kawai ya tsaya a ciwon kirji, ko rashin bacci ba ne ga manya.

Haka ga raya suna girma ciwon na kara yaduwa a jikin su, idan ba’a dauki matakan kariya ba tun da yarin ta. Duk mai ciwon na asma, ya kokarta wajen motsa jiki, don hakan nada matukar muhimanci. Cikin kashi 70% na mutane dake dauke da cutar, sukan kamu da wasu cututtuka da suke da alaka da cutar asma, da sukan zama kamar taki idan ba an magance su da gaggawa ba. Kusantar hayaki, da kura a lokacin yarinta na haddasa cutar matuka. Haka idan mace mai juna biyu na dauke da cutar, idan bata kare kanta yadda ya kamata, shima yana iya zama hanya da yaro zai kamu da ciwon.