Kamfanin Microsoft Da Hadin Gwiwa Zasu Fitar Da Sabuwar Manhaja

Kamfanin Microsoft da hadin gwiwa wani kamfani sadarwan zamani na Dynamiss Digital Learning Solutions Limited wadanda ke yin kayan karatu da koyarwa, zasu yi hadin gwiwa wurin kaddamar da wata manhajar koyarwa a aji mai suna “Dynamiss LP+365” wanda zai dogara da yanayin girgije, kuma zai zama hanyar sabunta manhajar “Microsoft Office 365” wanda zai saukaka yanayin karatu amakarantu, ya tsara darussan karatu, ya inganta yin karatu kuma ya nuna wa masu karatu hanya mafi sauki wurin dauka da ajiyewa a cikin manhjan.

Wannan sabuwar manhaja ta “Dynamiss LP+365” zata ba dalibai da sauran masu neman ilimi daman yin anfani da wannan hanya akoda yaushe, da kuma iya yin karatu bada taimakon wani ba, da kyautata yanayin sadarwa da yin hadin gwiwa.

Da yake tsokaci akan wannan manhajar shugaban reshen Microsoft a Nigeria, Jordan Belmote yace ilimin sadarwan zamani ba ayinshi don neman madadi ko annashuwa, sai dai ya zama ilimi mai muhhimmanci da mutum ke rayuwa dashi acikin wannan karni na ashirin da daya 21.