Kallo ya kare ga masoya wasan kwallo, a dai-dai lokacin da ake cikin tsakiyar wasa tsakanin gungiyar kwallon kafar San Jorge De Villa Elisa, da kungiyar Geronimo Quintana, duk a kasar Argentine. Sai dan wasa Michael Favre, ya samu haduwa da daya daga cikin abokan wasan na su, ana cikin maida magana, sai wani dan wasa ya sake bugen dan wasan nan take sai ya fadi a karo na biyu.
Shi dai dan wasan mai shekaru ashirin da hudu 24, ya mutu jim kadan bayan karon batta da su kayi, a lokacin da abun ya faru, daya daga cikin abokan wasan su, ya buge shi ya fadi, koda ya sake tasowa sai wani dan wasa kuma ya sake buge shi ya kai kasa. Daga nan bai sake tashi ba sai aka garzaya da shi asibiti.
A tabakin wani kamfanin labarai, dan wasan dai ya mutu, ya bar matar shi da ‘yaya biyu 2. Hukumar kwalln kafar kasar sun bayyanar da jimamin su ga iyalan mamacin. An dai nada kwamiti da zai binciki yadda abun ya abku.