Gwaggon Biri Yayi Garkuwa Da Yaro Dan Shekaru 4!

Gorilla Grauer

Wani yaro mai shekaru hudu 4, da haihuwa da ba’a bayyanar da sunan shi ba, ya fada cikin gidan “Gwaggon Biri” a gidan kallon namun daji na garin Cincinnati, a jihar Ohio, ta kasar Amurka. A dai-dai lokacin da wannan yaron da mahaifiyar shi suka, shiga gidan don ganin namun daji. Sai yaron yabi ta cikin wani karamin rami, sai cikin dakin gwaggon birai guda uku 3.

Gwaggon Birin da ake yima lakani da suna “Harambe” mai shekaru goma sha bakwai 17, yana da nauyin fan dari hudu 400. Jim kadan bayan yaron ya shiga ta wata karamar hanya. Sai birin ya kara jawo yaron cikin dakin shi, ya kwashe tsawon mintoci goma 10, yana wasa da yaron. Wani abu da ya kara tadama gwaggon birin hankali shine, yadda mutane keta ihu suna kiran taimako ga yaron.

Hukumomin gidan namun dajin, sun dauki wani mataki na kare yaron, wanda basuyi wata-wata ba, suka harbe gwaggon birin don ceto rayuwar yaron. Bayan dauko yaron an garzaya asibiti don duba lafiyar shi, duk da cewar ya samu raunuka a jikin shi.