Sun Yiwa Yaron Yankar Rago

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa wasu masu satar mutane sun sace wani yaro dan shekaru goma kuma sun yi masa yankar Rago.

Kakakin ‘yan Sandan jihar DSP, Magaji musa Majiya, ya yaron mai suna Musa Salisu, dan aji shida ne a makarantar firamari, an kuma sace shine a unguwar Naibawa, da misalign karfe biyu na rana a ranar litinin din da ta gabata.

Shi dai Musa, an aike shi ne cikin uguwarsu kafin a sace shi, kakakin ‘yan Sandan yace an kama wasu mutane biyu dagane da sace yaron da kuma aika aikan da aka aikata masa.

Kawun Musa, Malam Abubakar Kafinta, yace sai bayan misalin awowi uku, kafin a san cewa an sace Musa lokaci da wani ya yi waya ya sanar da iyayen game da faruwar lamarin.