Hattara Matasa! Ta Mutu Sanadiyar Zubar Da Ciki

Wata kotu a Ado Ekiti, ta bada umarnin a tsare wasu matasa biyu, Olarewaju Olorunfemi dan shekaru 21, da Sadiat Akeem, ‘yar shekaru 18, a bisa zargin hadin baki domin zubarwa Funbi Taiwo, ciki wanda yayi sanadiyar mutuwan ta.

Ita dai Funbi, budurwar Olarewaju, ce wanda kuma ake zargin cewa shine yayi mata ciki a cewar Sgt. Caleb Leranmo, wanda ya kasance mai gabatar da kara yace daga bisa Olarewaju da Sadiat wace kawar Funbi ce sun hada baki domin zubar mata da ciki.

A cewar mai gabatar da karar, wadanda ake zargi, sun aikata laifin a karkashin sashe na 319, sakin layi C 16, a kundin tsarin shara’ar jihar Ekiti, na shekara 2012, kuma tuni akara tura takardan shara’ar zuwa ofishin, daraktan shigar da kara na gwamnati domin bada shawara akan shara’ar.