An Rufe Kwalejin Ilimi Ta Gwamnatin Tarayya Dake Gombe

Kwalejin Ilimi na Gwamnatin tarayya Gombe

A jihar Gombe hukumar gudanarwan kwalejin ilimi na gwamnatin tarayya dake Gombe, ta rufe makarantar, biyo bayan tarzoma da daliban makarantar suka yi a yau dinnan a dalilin rashin ruwa da wutan lantarki.

Rahotanin na bayanin cewa daliban sun lalata gine gine da kuma motocin kwalejin wanda ya tilasawa jami’an tsaro yin amfani da bindiga da barkonon tsohuwa.

Kakakin hukumar ‘yan Sandan jihar Gombe DSP, Ahmed Usman, yace hukumar ‘yan Sanda na zaman ko ta kwana a makarantar, kuma yanzu haka akwai wasu dalibai yanzu haka a hannu.

Wani wanda a kayi abin akan idonsa ya shaidawa muryar Amurka cewa rikicin ya faru ne kan batun ruwa ne da wutan lantarki sun kuma kai kuka ga hukumar makarantar amma har yanzu batayi komai akan ba dalilin da ya jawo kennan kuma daliban sun lalata motocin malamai da dama. Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton babu bayanin wandada suka jirkata ko kuma na mutuwa.