Yau Ake Jana'izar Gwarzon Dan Dambe Muhammadu Ali

Muhammad Ali

Yau ake jana’izar gwarzon dan damben nan Ba’amurke bakar fata da ya yi fice a kasashen duniya Muhammad Ali.

Mohammad Ali dai ya sami karbuwa ainun a kasashen nahiyar Afrika saboda iya dambensa da kuma nemar wa bakaken fata 'yancinsu.

Mohammaed Ali ya kai wata ziyara ta tarihi a Yammacin Afrika, a shekarar 1964 inda magoya bayansa suka yi ta ihun kiran sunansa da yi masa kirari da “Sarkin damben duniya.”

Ziyarar tasa zuwa Afrika a 1964 ta zamo masa a bar tarihi, sakamkon nasarar da ya samu kan Sonny Liston, har ma ya zama gwarzon dan dambe na duniya, a kuma lokacin ne ya watsar da sunansa na bauta wato Cassius Clay, ya shiga addinin Musulunci.

(Ziyarar Muhammad Ali Zuwa Najeriya a 1971)

A shekara ta dubu da dari tara da casa’in da shida Mohammed Ali ya kai ziyara a Al-Kahira inda gwama siyasa da addini, lokacin da ya yi gaisuwar neman 'yancin bakar fata yayinda yake kabbara.

Fitacciyar ziyararsa zuwa Afrika ita ce a shekarar 1974 zuwa Kinshasa, babban birnin Zaire a wancan lokacin wato Jamhuriyar Dimokradiyar Congo a yanzu, domin wata gasar dambe.

Shugaban Zaire na wancan lokacin Mobutu Sese Seko ya amince ya biya dala miliyan biyar wadda take daidai da dala miliyan 24 a yanzu, ga kowanne dan damben da ya shiga gasar da aka yayata a akwatun talabijin da miliyoyin mutane suka kalla a duk fadin duniya.

Duk da yake Mohammaed Ali ba shine gwarzon wasan na duniya ba a lokacin, yayin da ya shiga da'irar yin wasan 'yan kallo sun barke da sowa suna masa kirari a yaren kasar kamar haka, "Ali, boma ye", wato ''Ali, lallasa shi.''. Ali ya kwace kambun duniya bayan ya yi nasara a kan George Foreman.

Mohammed Ali ya kai ziyara a Najeriya a shekara alib da dari tara da saba’in da daya zamanin mulkin Janar Yakubu Gowon.

Mohammed Ali, yace Na dauki wannan ziyarar da muhimmanci, a gaskiya an karrama ni, kuma ina godiya, domin ina da karfin jiki, amma ganinku da nayi, da kuma al’ummar, da yadda aka tsayar da ababan hawa, kamar shugaban kasa,wani abu ne da nake alfahari da shi.

Zan fadi gaskiya, hawaye ya zubo mani, da na fito kan titi naga ‘yan’uwana maza da mata yan Najeriya, kanana da manya da tsofaffi da matasa, wannan zai kara mani karfin guiwa idan na shiga motsa jikin horaswa.

Gowon yace masa yana tabbatar masa da cewa yana da magoya baya a Najeriya.

Mohammad Ali, yace “Nayi maku alkawari, da zarar an gama gasar,da zarar na sami kaina, zan dawo da matata da ‘ya’yana, muyi a kalla mako guda a nan da kuma mako guda a birni dake makwabta, Ibadan.

Mohammad Ali ya ziyarci Sudan a shekarar 1988, shekara hudu bayan da aka gano yana da cutar kyarma, domin ya isar da sakon Musulunci na addinin da ke son zaman lafiya. Ya yi sallah da addu'a a masallacin Sufi da ke birnin Khartoum.

Ya kuma kai ziyara a Afrika ta Kudu a shekarar alib dubu da dari tara da casa’in da uku bisa gayyatar Shugabannin addinin Musulunci bakaken fata na kasar Afrika Ta Kudu.

Mohammad Ali ya rasu makon da ya gabata, yana da shekaru saba’in da hudu.

Ya mutu ya bar matarshi, da ‘yaya tara da suka hada da Laila Ali fitattar ‘yar wasan dambe wadda ta zama zakarar damben mata ta duniya kafin tayi ritaya.