Masu iya magana dai kance “Babu nakasashe sai kasasshe” a karon farko, kasar Thailand, sun fito da wata gasa don bama yara makafi karfin gwiwar amfani da makantar su wajen zama wani abu a rayuwa.
Ita dai wannan gasar da aka fara a karon farko, an bama yara matasa dama su bayyanar da duk wata basira da Allah ya basu, wajen nuna bajintar su, da kuma irin gudun mawar su a kasar. Matasa da dama ne suka halarci wannan gasar, wanda wasu daga ciki suka bayyanar da tasu baiwar ta waka.
A kasar ta Thailand, akwai nakasassu kimanin milliyan daya da dubu dari takwas, wadanda daga ciki dubu dari da tamanin makafi ne. Yaran da suka halarci gasar sun fara daga shekaru takwas 8, zuwa goma sha biyar 15. Ansa makudan kudade ga duk wanda yaci gasar. Haka wadanda basu yi wani katabus ba an basu abun rikewa, saboda zuwan da su kayi.
A tabakin wadanda suka shirya gasar, sun bayyanar da wannan a matsayin wata hanya da za’a cire ma yaran damuwa, ganin suna da banbanci da sauran yara. Hakan kuma wata damace, da yaran zasu bayyanar da nasu irin baiwar da Allah, yayi musu. Suna ganin idan har sauran kasashe a fadin duniya, zasu dauki irin wannan tsarin don kaiwa ga nasu matasan, hakan zai taimaka sosai wajen rage bara da tumasanci a kasashe.