Shugaban Amurka, Obama Zai Karrama Sarkin Yarbawa Oba Adeyeye!

Sarkin Yarbawan Ile-Ife

Shugaban kasar Amurka Barak Obama, zai gana da sarkin Yarbawa Oba Adeyeye Ogunwusi II, biyowar bayan karrama shi da za’ayi, a matsayin mai garin babban birnin New York. An dai ware ranar 13, ga watan Yuli a matsayin ranar Yarbawa a kasar Amurka, don nuna al'adu.

Duk a yau ne shugaban kasa Obama, zai gana da sarkin a fadar “White House” ana kuma sa ran shugaban kasar zai karrama shi da lambar girmamawa, saboda irin gudun mawar yarbawa a kasar ta Amurka. Bayan nan kuma za’a gudanar da wasu bukukuwa a sauran sassa daban daban na kasar don murnan wannan girmamawar.

Sarkin kuma zai halarci wani bukin al’adun yarbawa da ake gudanarwa a kowace shekara, tun bayan kirkirar bukin da akayi a shekarar 1975, bukin kuma na samun halartar yarbawa sama da dubu dari biyar a kowace shekara. Ana kuma sa ran sarkin zai gana da ainihin ‘yan asalin masarautar Ile-Ife sama da dubu uku, mazauna kasar Amurka.