Duk Da Halin Rashin Akwai Wadanda Basu Jin Garin

Hauwa Muhammad Abdullahi

A yau mun waiwayi dabi'ar nan ta mata da suke yi na dafa abinci da yawa ko yaya suke yi idan hakan ya faru masamman a wannan wata mai alfama.

Mun sami zantawa da malama Hauwa Mohammad Abdullahi wacce ta bayyana mana cewar da zarar abincin buda baki ko na sahur ya ragu sai abinda ya kamata shine a gyarawa yara na gida da na makwabta.

Tace koda yake yanzu babu wadatar abinci kamar da, saboda haka zai yi wuya a diga dahuwar mai yawa da zai kai ga an zubar da abincin.

Tayi kira ga wadanda suka wadata da kada su manta da mabukata a kowane lokaci domin a cewarta duk da halin rashin da ake ciki akwai wadanda basu jin garin.

Ta kuma bada shawaran cewa wadanda ke zaune a wurare kamara GRA, da sauransu ya kyautu su diga fitowa da sauran abinci daga waje domin a cewar ta ko baya an sha ruwa za’a ga wasu mutane suna gararamba a titi suna neman abinci.