Matasa Sun Yi Zanga Zanga A Jihar Filato

Matasa a jihar Filato, sun yi wata zanga zangar lumana domin jan hankalingwamnati da ta cire sunan jihar Filato, daga cikin jerin jihohin da za’a kebe wuraren kiwo domin Fulani makiyaya.

Matasan da suka fito da sunan matasan Filato, sun sanya bakaken sitira kuma dauke da kwalayen da rubuce rubuce cewa “ a barmana kasa don yaran mu Filato bata da isasshen kasa don baiwa makiyaya bamu yarda da kwace filaye da sunnan kebe wuraren kiwo da dai sauransu.

Daya daga cikin matasan mai suna Rosemary Dalyop, tace yakamata kafin gwamnati ta dauki mataki akan wannan batu ya kasance sun samu tattaunawa da masu gonaki tukunna.

Ta kara da cewa idan har aka samu tattaunawa da masu gonakin duk wanda ya amince sai ayi ciniki.

Daraktan inganta zaman lafiya na jihar Filato, Joseph Lengman, yace gwamnati na kan tattara bayanai domin duba lamarin, yana ganin cewa akwai rashin ganewa watakila akwai yadda akayiwa maganar fasara da mutane basu fahimta sosai ba.

Yakara da cewa har yanzu suna fadi da babbar murya cewa gwamnati bata riga ta dauki mataki akan batun bane, har yanzu zance ne ake yi akai agani ko zai yu ko bazai yuba.