Ba Da Gudumuwar Jini Domin Ceton Rayuwa

Dr. Aisha Kuliya Gwarzo

Hukumar lafiya ta duniya lafiya dai ta ware 14 ga yunin kowacce shekara tun 2004 a matsayin ranar bikin bana gudumuwar jini na sa kai don inganta harkokin lafiya tare da inganta samar da jini na kyauta a kowacce kasa ba tare da an tursasa mutum ya bayar ba wanda zai taimaka wajen ceto wasu rayuka

Taken ranar a bana dai shine, dangantaka ta jinni ,ka ba da gudumuwar jini domin ceton rayuwa ,na nuni da cewar tallafin jini na kara dankon zumunci tare da hadin kai alumma.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ce Kimanin mutane miliya 108 ne a fadin duniya ke ba da gudumuwar jini a duk shekara,yayin da kaso hamsin na wannan adadi ke fitowa daga kasashen da suka cigaba.

A Najeriya, kuwa kaso goma cikin dari ke bada gudumawar jini na sa kai wanda ya saba da kudirin hukumar lafiya ta duniya.

Dagane da haka ne wakiliyar muryar Amurka, Baraka Bashir, ta tuntubi Dr. Aisha Kuliya Gwarzo, wace tace kowa zai iya bada jini ko mace ko namiji, amma kafin a yarda mutun ya bada jini sai an tabbatar da yawan sa ajikin mutun da kuma lafiyar jinin.

Idan mace tanada juna biyu ko kuma tana alada ko kuma tana shayarwa ba’a bukatar ta bada jini, banda wadannan dalilai mace na iya bada jini karmar sau biyu zuwa sau uku a shekara namiji kuwa har sau hudu zai iya badawa.