Muhimmancin Hakuri Da kuma Tsaka Mai Wuya Da Mata Ke Ciki

A yau dandalin VOA ya samu zantawa da mata ne dangane da muhimmancin hakuri a watan Ramadan, inda Malama Zahr'u na hukumar hisbah tayi mana fashin baki akan hakuri a wannan lokaci cikin wannan wata mai alfarma.

Malama Zahr’u, tace kusan jama’a ba’a fahimci menene Azumi ba, tace shi Azumi, wata rahama yake sawa a cikin zuciya da kwanciyar hankali da rashin tashin hankali, so ake kullum ya kasance cewar zuciyar ka cikin dadi take.

Tana mai cewa a cikin watan Azumi jama’a afi yi fada akan titi saboda rashin hankali da rashin hakuri, ta kara da cewa shi azumi garkuwa ne daga duk garari baki daya.

Daga bisa ni kuma mun sami zantawa da wata ma'aikaciya wace ta yi mana bayani yadda suka dawaini da harkokin gida , maigida da yara , a hannu guda kuma su je wuraren ayyukansu domin yin aiki yadda aka saba.

Tace aiki a wurin mace ga maigida ga yara ga kuma zuwa wurin aiki wallahi ba karami tsaka mai wuya take ciki ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Mahimmancin Hakuri Da kuma Tsaka Mai Wuya Da Mata Ka Ciki - 3'18"