Bashi Na Jawo Nakasu Ga Kowace Sana'a

Uzairu

A yau mun waiwaye batun sana'a ne a watan Ramadana , inda muka zanta da wani matashi Uzairu, mai sana’ar sayarda Kadin waya da sauran kayayyakin waya.

Ya kuma cewa , a wannan lokaci shi dai sai ya ce sambarka,domin a yan kwanakin nan kasuwa ta na kyau sai dai yan abinda ba'a rasa ba da suka danganci batu na bashi.

Uzairu, ya kara da cewa mutane na karbar bashi kuma biyart sai ya zama wani sabon Magana abin nufi shine bashi na dan jawo nakasu ga harkar kasuwanci kowane irin ne idan har masu karban bashi basu biya akan lokaci.

Ya ce yana fara sana'oinsa tun daga karfe takwas na safiya har zuwa sha biyu da rabi na dare sakamakon hada hadar alumma a wannan watan.

Your browser doesn’t support HTML5

Bashi Na Jawo Nakasu Ga Kowace Sana'a - 2'17"