A jamhuryar Nijar, wasu matasan ‘yan jarida da suka kammala karatu a makarantar horon ma’aikatan watsa labari sun fara bitar a wani matakin tantance wadanda suka cancanci samun takardar shedar kammala karatun.
Matasan fiye 100, maza da mata sun fito ne daga kasashen Niger, Chadi,Gabon, da wadanda suka fito daga kasashen yammacin Afirka, masu amfani da harshen Faransanci, da suka kamala karatu a fannoni daban daban na aiyukan watsa labarai a makarantar IFTIC.
Wadanan dalibai sune ke bitar abinda suka karanta na tsawon shekaru uku, wanda ke matakin karshe kafin samun shedar kammala makarantar.
Daliban da suka gabatar da tasu bitar a farkon wannan kwarya kwaryar jarabawar sun nuna farin ciki da nasarar da suka samu.
Your browser doesn’t support HTML5