Za'a Yi Gumurzu A Fagen Kwallon Kafa

Neymar Dan Brazil

A ci gaba da gasar Olympic a kasar Brazil, a bangaren kwallon kafa na maza an fafata a wasani da dama ida a rukunin “A” Brazil da Iraqi, suka tashi babu ci Denmark ta sami nasara akan Afirka ta Kudu da ci daya da nema a wannan rukuni Denmark nag aba da maki ukku, Brazil na biye da ita da maki biyu yayin da Iraqi, nada maki biyu Afirka ta Kudu nada maki daya.

Ranar Alhamis idan Allah ya kaimu 11, ga watan nan damuke ciki Denmark zasu fafata da kasar Brazil, yayin da Iraqi zasu fafata da kasar Afirka ta kudu.

A rukunin “B” kuwa Najeriya, ta sami nasara akan Sweden, da ci daya mai banhaushe Japan sun tashi biyu da biyu da Columbia, Najeriya ta sami zuwa zagaye nag aba da maki shida yayin da Columbia ke biye da ita da maki biyu Japan da maki daya itama Sweden nada maki daya.

Najeriya zasu fafata da kasar Columbia ranar laraba , Japan zasu yin karon bata da Sweden.

A rukunin “C” kuma Mexico ta lallasa Fiji Island, da kwallaye biyar da daya Koriya ta kudu sun tashi ukku da ukku da Jamus, Koriya ta kudu nag aba da maki hudu, Mexico na biye da maki hudu, Jamus nada maki biyu Fiji Island na neman maki..\Koriya ta kudu zasu fafata wasan su ranar laraba da kungiyar kwallon kafa ta Mexico Jamus zasu buga da Fiji Island.

A rukunin “D” Portugal ta samu nasara akan Honduras da ci biyu da daya yayin da Algeria ta sha kasha a hannun Argentina, da kwallaye biyu da daya Portugal ta sami zuwa zagaye na biyu inda take da maki shida Honduras nada maki ukku itama Argentina maki ukku, Algeria na nema.Ranar laraba idan Allah ya kaimu Portugal zasu fafata da Algeria inda Argentina zasu buga da Honduras.

Your browser doesn’t support HTML5

Za'a Yi Gumurzu A Fagen Kwallon Kafa - 2'09"