Ba Ai'bu Ba ne Matsawar Bai Saba Al'ada Da Addini Ba

Jamilu Yakasai

Shugaban kungiyar masu shirya fina-finan na arewacin Najeriya, reshen jihar Kano, Jamilu Yakasai, Yace a karkashin sabon shugabancin kungiyar za’a tabbatar ganin cewa an tattance duk masu bukatar shigowa harkar fina finai.

Ya furta haka ne a tattaunawarsu da wakiliyar dandalinvoa Baraka Bashir, inda ya kara da cewa a yanzu haka kungiyar na maida duk wanda kungiyar ke da tababa akan izini iyayesu na fara harkar fina finai inda sau tari kungiyar ke kira iyayen ta wayar taliho, ko kuma su maida su masamman mata.

Ya ce kawo yanzu sun daura damara dakile duk wanda yake kawo kace-na-ce ga harkar fina-finai domin canjin da ya kamata, ya ce babu tantama akan sami wadanda ke shiga masana’antar ta bayan gida, a yanzu lokaci yayi da kungiyar ke kokarin dakile wadanan matsaloli.

Ya kara da cewa batun sanya rawa a fina-finansu ba ai'bu ba ne matsawar bai saba al'ada da addini ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Ai'bu Ba ne Matsawar Bai Saba Al'ada Da Addini Ba - 4'45"